May 22, 2024

Table of Contents

Y’AN MATA RETURN….

By Hafsat Hisham

(AYSHER ANGEL)

Page 62 and 63

Zanyi maku posting dinshi daga farko har karshe a free, except for wadanda suke son complete
For wadanda suke son complete dinsa zasu samu akan naira dari ukku 300, kuyi min magana ta pc kuyi payment in tura maku
Hafsat tace, “No, waccen ranar na tuna…”.
Aliyu yace, “Nima zan rama… Shine kikazo babu notice babu komai, dubi yadda kika sameni har naji kunya…”.
Hafsat ta kalleshi yana sanye ne da wasu kananan kaya amma sun sha jiki, tayi dariya sannan tace,
“Gani ya kori ji kadda in auri k’azami ban sani ba…”.
Aliyu ya ware idanu, Hafsat tace,
“Wasa nike maka, Ummy ce ta aikeni shine na biyo ta nan in ganka tunda kayi min hijira…”.
Aliyu yace, “Ba haka bane, dinkuna ne sukayi min yawa shiyasa amma kullum kina raina…”.
Hafsat tace, “Kace kullum ina ranka, amma shine babu kira babu text message babu ziyara, kuma gaske kake…”.
Aliyu yace, “Hafsat kiyi hakuri bani da kudi ne…”.
Hafsat tace, “Ni kuma bana kiran samari, muje ka rakani, da fatan ka iya mota…”.
Aliyu ya girgiza kai sannan yace,
“Hafsat ban iya mota ba…”.
Hafsat ta ware idanu tace,
“Katon saurayi da kai amma kace baka iya mota ba, kaga k’anin Amatullah duka jss three yake amma ya iya mota…”.
“Ba abun mamaki bane don nace ban iya mota ba, wanda kika fad’a daban ni daban, shi akwai motoci a gidansu, ni kuma gida babu, a neighbor babu, abokai basu dashi kinga kuwa ai babu mamaki domin nace maki ban iya ba…”.
Hafsat ta ware idanu tareda dafe kai tace,
“Hakane, zan koya maka daga yau…”.
Aliyu ya ware idanu, tace,
“Yeah if not inyi zuciya…”.
Yace, “Na tuba…”.
Tace, “Gwara ka tsaya in koya maka…”.
Yace, “Dole, kadda kiyi fushi dani, in rasa inda zan saka kaina…”.
Hafsat tayi dariya sannan tace,
“Lokaci yana wucewa kadda Ummy taga na makara, ka zagaya ka shiga muje, tunda baka iya mota ba sai ka hau tukin mace…”.
Aliyu ya kalleta tayi fari da idanu tareda gyad’a kai, ya zagaya ya bud’e bangaren mai zaman hakanan ya shiga, taja motan tana driving a nutse yayinda baki daya hankalinta yake akan titi, ji tayi yace,
“Lovely, kinyi kyau, Angel…”.
Hafsat tace, “Babu wani nan nayi wanka na wanku amma baka yabani ba sai yanzu, ban yarda ba, wannan duk bige ce, next time idan kana ganina ka yaba sai in yarda amma yanzu babu wannan maganar…”.
A daidai wasu manya-manyan shaguna tayi parking ta fito ta wuce ciki tana rik’e da katuwar leather ta jima sosai sannan ta fito tareda wata er budurwa fara daga ganinta ta had’a jini da kasar ketare, tana da kyau fiye da tunani, suna tafiya suna dariya har suka karasa, er budurwar ta kalli Aliyu tace,
“Angel tare kike da driver…”.
Hafsat tayi dariya sannan tace,
“Yeah Jawaheer tare nike da driver… Ehhh direbana ne tunda idan munyi aure dole yayi driving dina tunda ba yaso inyi wahala… He is my boyfriend, Aliyu…”.
Jawaheer ta ware idanu sai kuma tayi murmushi sannan tace,
“Of course… Aliyu, ya kake, ya aiki, ka kula mamu da Angel, banda bata ciwon kai, idan tace fad’a rijiya, kawai ka fad’a…”.
A tare sukayi dariya har dashi, tace,
“Hafsat zan koma, bye, sai na kawo maki invitation card…”.
Hafsat tace, “Alright, sai kin zo…”.
Jawaheer ta juya ta koma ciki, Hafsat ta kalli Aliyu ta fashe da dariya, yace,
“Zaki fara ko?”.
Tace, “Shiga muje daga yau zaka fara daukar darasi akan driving har sai ka kware, ka wuce masu lodin Abuja da Lagos…”.
Tana driving, Aliyu yace,
“Ashe dinki zaki kawo amma shine baki bani ba”.
Hafsat tace, “Wannan dinkin na Ummy ne, kaga wannan yarinyar tunda muka tashi muka tarar mamarta tana wa Ummy dinki, rayuwarsu abun tausayi, mahaifiyar ta auri wani d’an kasar waje, ya nuna mata matanshi ukka itace ta hudu, ashe yaudararta yayi, sunyi shekaru har sun haifi diya daya Jawaheer, Allah yayi mashi rasuwa, tana zuwa kasarsu ta tarar ashe matanshi hudu itace ta biyar, bata da gado hakanan diyarta, babu d’ad’i sukayi mata ta dawo kasarnan ta rungumi diyarta tana mai cigaba da harkar dinki da takeyi tuntuni, duk da akwai ciwo a rayuwarta amma bata yarda wannan ya hanata farin ciki ba, hakanan erta baki dayansu sunyi tawakkali, sau biyu ana yima Jawaheer engagement yana watsewa amma yanzu ta samu wani wanda yace yaji ya gani zai aureta a yadda take, bata da laifi hakanan mahaifiyarta, shine kaji tana cewa sai ta kawo min invitation card, k’awata ce…”.
Aliyu yace, “Ayyerh sun bani tausayi…”.
Hafsat tace, “Ai dole, basu da laifi amma laifin wani yana bibiyarsu…”.
Aliyu yace, “Allah ya kyauta…”.
Hafsat tace, “Amin…”.
Tun daga wannan rana ta fara mashi driving, kullum zata zo ta daukeshi tana koya mashi tuki har ya kware, hannunshi ya zauna sosai….
*********
Aliyu yana kiranta tana ganin kiran tayi banza dashi, saida ya gaji don kansa ya daina kira sannan ta tura mashi text message….
“Idan ka mance hanyar gidanmu ne sai in k’ara maka kwatance….”.
Ta kashe wayar baki daya tareda tab’e baki….
FatimaZahra tace, “Miye?”.
Hafsat tace, “Aliyu ne, haushi yake bani, kusan sati guda, babu ziyara, ya barni sai kace wacce bata da saurayi…”.
Amatullah tace, “Ayyerh watakila bashi da kudi shiyasa… Wannan shine dalilin da ya saka muke rabaki da soyayya da talaka amma kin manne mashi…”.
Hafsat tace, “Duk da ban tab’a soyayya da talaka ba amma abun Aliyu akwai careless, rashin kudi wannan ba dalili bane ai yana dinki babu yadda zaice kudin transport sunfi karfinshi… Ai ya bani haushi…”.
Bayan sallar isha’i, tana zaune parlour ita da Hisham suna hira, daya daga cikin maid tace,
“Hajiya kina da bako a garden…”.
Hafsat tace, “Okay…”.
Ta mik’e tsaye tareda zura takalma flat, gown ce a jikinta, ta warware veil dake saman kanta tayi rolling dashi, tabi ta kofar baya dake manne da kitchen tayi appearing a garden, ta zauna kujerar dake opposite dashi, ya zuba mata idanu saying,
“You look lovely, Angel…”.
Hafsat fuskarta a murtuke tace,
“Ashe baka manta hanyar ba…”.
Aliyu yace, “Hafsat kiyi hakuri abun da ya faru shine…”.
Hafsat ta katseshi tace,
“Don’t, kadda ka b’ata min rai kaima ranka ya b’aci, magana ta wuce, duk wanda yayi daidai ya sani hakanan wanda yayi akasin hakan saidai mutum ya take sani…”.
Aliyu yace, “Alright… Da fatan kina lafiya?”.
Tace, “Lafiya lau and you…”.
Yace, “Lafiya lau nike saidai kewarki da nayi…”.
Tace, “Ay gani nan gabanka…”.
Yace, “Hakane kuma kinyi kyau, what about me?”.
Tace, “Duhu ne bana tantancewa…”.
Yace, “In haska maki?”.
Tace, “A’a…”.
Yace, “Alright…”.
Tace, “Alright…”.
Yace, “Gobe idan Allah ya kaimu zanzo da marece…”.
Tace, “Better…”.
Yace, “Zan tafi…”.
Tace, “Ba yanzu ba…”.
Yace, “Abun da kika ce shi zanyi…”.
Tace, “Good…”.
Imran ne daya daga cikin siblings din Amatullah ya kawo mata kit saying,
“Gashi Yaa Nafiu yace in kawo maki…”.
Hafsat tace, “Wow… Na gode sosai, Imran tare kake dashi…”.
Imran yace, “Ehhh yana bakin get…”.
Hafsat tace, “Alright, kace mashi na gode sosai koda yake tsaya in baka tukwuci…”.
Aliyu yace, “Barshi in bashi…”.
Sai kuma ya zaro naira hamsin wadda ita kadai ce ta rage mashi ya mik’a mashi, Imran yayi sororo yana kallonshi tareda naira hamsin din, Hafsat ta kalli reaction din Imran ta fashe da dariya, tace,
“Imran rabu dashi tsokanarka yake, jeki wurin Yaa Hisham yana parlour kace mashi nace ya baka five thousand naira…”.
Imran ya wuce ciki, Hafsat ta kalli Aliyu ta fashe da dariya, Aliyu yace,
“Ya dai…”.
Imran ne ya dawo yace,
“Kin gani ya bani 10K…”.
Ya fad’i yana nuna mata sabbin en dubu daya-daya dake hannunsa, Hafsat tace,
“Kace wa Yaa Nafiu na gode sosai…”.
Imran ya gyad’a kai har ya soma tafiya ya dawo da baya yace,
“Angel ki fad’a mashi ni ba yaro bane…”.
Hafsat tace, “Sure, I will…”.
Imran ya wuce, Hafsat ta kalli Aliyu ta fashe da dariya, tace,
“You know what da ka bashi naira hamsin ji yayi it either ka daukeshi yaro ne sosai ko kuma tsokanarshi kake…”.
Sai kuma ta fashe da dariya ya jima sannan yayi mata salaam ya wuce, saida ya taka a kafa ya rage tafiya sannan ya tsaida achaba ya kaishi gida a naira hamsin wadda itace last kobo da yake da…..
Hafsat tana shiga ciki ta zauna a parlour, Hisham yace,
“Yaushe zakije shopping da saurayinki?”.
Hafsat tace, “Ban zuwa shopping…”.
Hisham yace, “Zan baku kudin shopping…”.
Hafsat tace, “A’a, mun yafe…”.
Ummy tace, “Barshi tsokanarki yake don nace mashi gobe zamuje shopping…”.
Hafsat tayi murmushi tareda hugging dinshi, Ummy ta daka mata tsawa tace,
“Ke…”.
Hafsat tayi firgigit ta sakeshi ta mik’e ta wuce bedroom dinta ta zare gown dake jikinta ta d’aura towel ta wuce bathroom ta jima tana wasa da kumfa sannan ta sakarwa jikinta shower ta fito daga bathtub tareda d’aura towel tayi brush sannan ta d’auro alwalla ta fito ta saka wata half night gown mai shara-shara kamar matacin koko wadda da ita da babu duk daya, saida ta feshe jikinta da perfumes sannan ta tofe room din da addu’a, tayi light off tabi lafiyar gado tareda jan blanket ta rufe daga kafafunta har zuwa saman kirjinta sai kuma ta janyo wayarta ta danna mashi call, tayi jim sannan tace,
“Da fatan ka isa gida lafiya… Haka ake so… Kadda kazo gobe… No, zamuje shopping da Ummy… Ban sani ba… No… Ka bari sai washegari… Watakila… Kaine kake nema ka b’ata min rai… Ya wuce… Alright… Allah yasa… Bye…”.
Sai kuma tayi hanging call din tareda mayar da wayar akan bedside drawer, ta lumshe idanu babu b’ata lokaci bacci yayi awon gaba da ita….
Washegari,
Ummy ta gama shiri ta zura long hijab ta dauki poss yayinda Hafsat ta shirya cikin leshe dinkin riga da skirt, ta yafa veil a shoulder, simple makeup ce a fuskarta amma tayi matuk’ar kyau looking breathtaking, suka fito Hafsat tana shagwab’a suka shiga mota, Ummy ce take driving yayinda Hafsat take zaune bangaren mai zaman hakanan tana buga game, tayi parking bakin wata katuwar shopping mall suka fito, tunda suka shiga ciki hankalin samari ya dawo akan Hafsat amma babu chance tare take da Umminta, shopping sukayi sosai inda Hafsat ta zage ta debi kaya sosai amma koda tsinke bata daukarwa Hisham ba, tayi fushi saboda tace suzo tare yace a’a aiki, wata expensive wristwatch ta gani, a take ta hango yadda zatayi kyau a hannun Aliyu don haka babu b’ata lokaci ta daukar mashi, suka gama aka yi masu bill Ummy ta biya, aka saka masu kaya a manya-manyan leather aka bisu dasu har mota aka saka masu a backseat, Hafsat ta shagwab’e fuska sannan tace,
“Ummy key inyi driving…”.
Ummy ta dubeta ta girgiza kai saying,
“Ungo…”.
Hafsat ta mik’a hannu, Ummy tace,
“See you, shige muje, sai in baki key kiyi driving dina tunda bani hannu, oya shige muje…”.
Hafsat ta zagaya daya bangaren yayinda Ummy ta shiga bangaren direba, tayi wa motar key idanunta akan titi, tace,
“Hafsat baki jin magana ko… Ni kike cewa in baki makulli kiyi driving dina tou bari kiji tun kafin in haifi Hisham nike driving mota…”.
Hafsat tayi dariya sannan tace,
“Ummy ai mu sabon hannu ne, ku kuma tsohon hannu…”.
Ummy tace, “Hafsat wato ke da Hisham kun mayar dani kakarku…”.
Hafsat ta fashe da dariya sannan tace,
“Aahhh ai granny dinmu tana Mahuta… Ummy ba nan bane hanyar gida…”.
Ummy tace, “Na sani zamu biya ne gidan Deenerh…”.
Hafsat tace, “Gidan Aunty Deenerh, Allah yasa Kausar tana gida…”.
Zanyi maku posting dinshi daga farko har karshe a free, except for wadanda suke son complete
For wadanda suke son complete dinsa zasu samu akan naira dari ukku 300, kuyi min magana ta pc kuyi payment in tura maku

FREE DOWNLOAD

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete Y’AN MATA RETURN

The most reliable and easiest way to obtain the complete Y’AN MATA RETURNisto purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete Y’AN MATA RETURNin Portable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the complete Y’AN MATA RETURN booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an email containing the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

Related Posts
Dowload Abban Sojoji Hausa Novel: Complete Popular Book 1, 2 3 and Reviews

Abban Sojoji is a popular Hausa novel written by Hafsat Bature, also known as Boss Lady. The novel tells an Read more

Dowload Kalaman Soyayya Hausa Novel Complete PDF

  A--Agaskiya ina sonki. B--Babban burina na aureki. C--Cuttar sonki batada magani a gurin likita. D--Daddadan lafazinki kan sanyayamin rai. Read more

Dowload Alkawarin Macijiya Hausa Novel Complete PDF

Alkawarin Macijiya is a popular Hausa novel that has gained a lot of attention in recent years. The novel tells Read more

Download A SANADIN MAKWABTAKA Hausa Novel Complete PDF

A SANADIN MAKWABTAKA is a popular Hausa novel that tells the story of a young woman named Aisha who falls Read more

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

65d48F